Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Cimma muradun karni a Afrika

Image caption Samar da abubuwan more rayuwa na kan gaba a cikin maradun na Majalisar Dinkin Duniya

Yayinda ya rage shekaru 5 na cimma muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya, abin tambayar shi ne shin Afrika za ta iya rage yawan mutanen da ke rayuwa cikin kangin fatara ya zuwa rabi nan da wa'adin shekara ta 2015.

A wajen taron kolin da aka yi a shekara ta 2002, rage yawan mutuwar yara da samar da ilmin Furamare kyauta ga kowa da kowa da kuma inganta kula da lafiyar mata masu juna biyu na daga cikin muradu 8 a kan agendar taron.

A halin yanzu shekaru 10 daga bisani, shugabannin duniya sun yi taro a New York domin sake nazartar yanayin.

A wajen bude taron kolin na baya bayan nan Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya,Ban Ki Moon ya ce bai kamata kasashe su yi amfani da koma bayan tattalin arziki a matsayin wata dama ta rage bayar da agaji ba. Akwai dai shedar da ke nuna cewar kasashen Afrika da dama sun samu 'yar nasara a wajen cimma muradun karnin.

Alal misali kasar Ghana ta rage yawan mutanen da ke fama da tamowa da kashi 75 cikin dari tun daga shekarar 1992. A halin yanzu kashi 8 cikin dari na al'umar ta ne kawai ke da matsalar abinci mai gina jiki.

Dangane da kokarin Najeriya kan cimma wadannan muradu kuwa, Shugaba Goodluck Jonathan ya shedawa Babban taron na Majalisar Dinkin Duniya cewar, ya zuwa yanzu Najeriyar ta tasamma ci gaba mai gamsarwa wajen rage fatara, kodayake kasar na kan hanyar cimma wasu daga cikin muradun karnin nan da shekara ta 2015.

Ya ce, Najeriya za ta samu nasarar cimma abinda ake bukata a kan rage mutuwar yara kananan da samar da ilmin Furamare ga kowa da kowa, to amma fa tana fuskantar wani babban kalubale a fannonin yin mu'amala da sauran kasashen duniya wajen raya kasa da mutuwar mata masu juna biyu da kuma a kan muhalli.

To domin tattaunawa kan batun mun gayyato baki da suka hada da Hajiya Amina Azzubair, Mai baiwa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin da suka shafi muradun karnin wadda yanzu haka take a birnin New York wajen babban taron Majalisar dinkin duniya.

Akwai kuma Dr Husaini Abdu, na kungiyar Action Aid mai zaman kanta, sannan muna tare da Madame Yaro Asma Ghali, Darakta mai kula da lafiyar mata da kananan yara a Ma'aikatar lafiya ta Jamhuriyar Nijar, sannan akwai Alhaji Alhassan Abdullahi, Shugaban wata kungiyar neman samar da ci gaba mai dorewa mai zaman kanta.