An sabunta: 6 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 20:56 GMT

Ra'ayi Riga: FIFA ta dakatar da Najeriya a fagen kwallon kafa

Super Eagles na Najeriya

Super Eagles na Najeriya

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya wato FIFA, ta dakatar da Najeriya daga shiga duk wata gasa, ko da kuwa ta sada zumunci ce.

Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda katsalandan din da ta yi zargin gwamnatin Najeriya na yi a cikin harkokin hukumar kula da kwallon kafa ta kasar NFF.

Shin wannan mataki ya dace? Kuma ta yaya zai shafi makomar Najeriya a fagen wasan kwallon kafa a nan gaba?

Wannan shi ne batun da za mu tattauna a kai a cikin shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

Domin shiga shirin sai ku aiko da takaitaccen ra'ayinku da kuma lambar wayar ku, ta e-mail a hausa@bbc.co.uk, ko ta lambar da aka saba wato 00447786202009 ko kuma ta dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara wato BBC Hausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na BBCHausa.com.

Za kuma ku iya bayyana ra'ayin naku a gurbin da ke kasa:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.