An sabunta: 20 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 12:02 GMT

Ra'ayi Riga: Shin za a iya kawar da zazzabin cizon sauro nan da shekaru biyar?

Sauro mai haddasa cutar Malaria

Sauro mai haddasa cutar Malaria

Zazzabin cizon sauro kamar yadda alkaluma suka nuna, yana hallaka akalla mutane miliyan guda a duniya a kowacce shekara, galibi a kasashen Afrika.

Rashin tsaftar muhalli na daga cikin al'amuran da ke rura wutar matsalar.

Shin yaya kuke ji da zazzabin cizon sauron?

Kuma a ganinku, ko za a iya kawar da shi nan da shekaru biyar masu zuwa kamar yadda aka zayyana a muradun karni na majalisar dinkin duniya?

Muna sauraronku a filin Ra'ayi Riga na wannan makon.

Sai ku aiko mana da takaitattun ra'ayoyinku da lambar wayar da za mu tuntube ku a kai, ta adreshinmu na email wato hausa@bbc.co.uk ko ta dandalin mu na muhawara, wato BBCHausa Facebook wanda za ku iya samu a shafinmu na internet wato bbchausa.com ko kuma ta lambar wayar nan da aka saba wato: 44 77 86 20 20 09.

Za kuma ku iya aiko mana da ra'ayinku ta gurbin da ke kasa:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.