Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin Nijar

Image caption A watan Fabreru za a gudanar da zabe domin maida mulki ga farar hula

A jamhuriyar Nijar, ranar Lahadi ne za a gudanar da kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki a ci gaba da shirye-shiryen da ake na maida kasar kan tafarkin dimokradiyya.

Tun bayan da Majalisar mulkin sojan Nijer ta CSRD, karkashin jagoranci Janar Salou Djibou ta hau kan karagar mulki a ranar 18 ga watan Fabrairun da ya gabata, ta dauki alkawarin mika mulki ga hannun farar hula.

Wannan kuriar raba-gardama da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa dai, ita ce matakin farko na shirye-shiryen da gwamnatin mulkin sojan Nijar din ta yi na maida kasar kan turbar Demokradiyya.

Zaben na rabagardama zai tantance ainihin nasara ko akasin haka a sauran zabubbukan da za a gudanar a nan gaba, ciki har da na shugaban kasa, wanda za a yi ranar 31 ga watan Janairu na badi.

Shi dai wannan sabon kudin ya tanadi tsarin mulki ne mai ruwa biyu, inda shugaban kasa yake raba iko da Pira Minista.

Shin ko wannan tasrin mulki ya dace da yadda al'amura suke a jamhuriyar ta Nijar? Kuma shin jama'a sun fahimci tanade-tanaden tsarin mulkin?

To domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato baki da dama domin shiga cikin shirin wadanda suka hada da Malam Ben Omar Mohammed na kawancen jam'iyyun AFDR wadanda suka yi mulki kafin sojoji su kwaci iko.

Da Malam Bazoum Mohammed na kawancen jam'iyun CFDR wadanda suka yi adawa da mulkin tsohon shugaba Mamadou Tandja.

Sannan kuma akwai Dr Soule Hassan, malamin tarihi a jami'ar Poitiers dake Faransa, kumai mai sharhi kan al'ammuran yau da kullum.

Akwai kuma masu saurare dake kan layi wadanda suka bayyana ra'ayinsu kan wannan batu.