Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Al'adar bikin aure

Image caption Yadda mata ke dafa abinci a lokacin bikin aure

A wani rahoto da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta buga da hadin guiwar, asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da babban bankin duniya a watan Satumbar da ya gabata.

Ya bayyana cewa yawan mace-macen mata da kananan yara ya ragu da kashi 34 cikin dari a fadin duniya baki daya.

Sai dai wannan raguwar bata shafi nahiyar Afrika ba, domin rahoton ya nuna cewa a shekarar 2008, a kullum mata 1000 ne ke mutuwa a sanadiyyar matsalolin da suka danganci goyon ciki a fadin duniya.

Kuma sama da mata 500 ne cikin 1000 da ke mutuwar a kullum na kasashen Afrika ta kudu da sahara.

A kudancin Asiya mata 300 ne daga cikin 1000 da ke mutuwa a kullum. Yayinda a kasashen da suka ci gaba kuwa mata biyar ne ke mutuwa a kullum a shekarar ta 2008.

Talauci da al'ada

Masana a fannin kiwon lafiya dai sun yi ittifakin cewa matsalolin da ke janyo yawan mace macen mata masu juna biyu dai abubuwa ne da za'a iya kaucewa.

Image caption Bikin aure wata dama ce ta sada zumunta tsakanin jama'a

Talauci da wasu al'adunmu da rashin ilimi gami da rashin kyakkyawan shugabanci na daga cikin dalilan da rahoton yace suka sa cimma muradun karni na rage mutuwar mata masu juna biyu da kashi uku cikin hudu nan da shekarar 2015 zai yi wuya a nahiyar.

Shirin Haifi ki yaye da BBC Hausa zai sanya tubali na duba irin wadannan matsaloli da zimmar samo bakin zaren.

To shirin haifi ki yaye da BBC Hausa ya yi shimfida da yadda ake aure a tsakanin wasu al'umomi domin aure shi ne hanya karbabba na samar da zuriya ga malam Bahaushe har ma da wasu al'umomi a fadin duniya.

Wakilanmu a Maiduguri Bilkisu Babangida da Tchima Ila Issoufou sun duba mana yadda ake bikin aure a jihohin maiduguri a Najeriya da kuma Maradi a Nijar.

Yayinda Nafisa Ahmed ta duba mana yadda al'amuran auren ke gudana a tsakanin mutanen Fasha na kasar Iran.