Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zubar da ciki ta haramtacciyar hanya

Image caption Wata mace na jimamin mutuwar 'yar uwarta ta hanyar zub da ciki

Kwararru sun bayyana cewar kimanin mata dubu sittin da bakwai ne ke mutuwa a kowacce shekara wurin zubar da ciki ta haramtacciyar hanya, kuma yawancinsu daga nahiyar Afrika suke.

Sama da rabin matan da ke rasa ransu a Afirkar a lokacin zub da cikin, basu kai shekara ashirin da biyar ba.

An kuma bayyana cewa, mata miliyan biyar ne ake kwantarwa a asibiti a kowacce shekara, a dukan fadin duniya, saboda matsalolin da ke biyo bayan zubar da ciki. Fiye da miliyan guda daga cikinsu a nahiyar Afirka.

To shin yaya matsalar take a kasashen na Afrika irinsu Najeriya, Nijar, Kamaru da Ghana?

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato Sheikh Huseini Zakariya, wani mai wa'azi na addinin Musulunci; da kuma Reverend Jacob Babale, malamin addinin Krista.

Muna kuma tare da Dr Hauwa Musa Abdullahi likitar mata a asibitin Murtala a Kano; da kuma Hajiya Hadiza Na-gona, babbar darektar kungiyar GHON mai zaman kanta, mai kula da lafiyar da ta shafi haihuwa da kuma yaki da talauci.