Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tarnakin biyan sabon albashi a Najeriya

Image caption Yadda titi ya dade a lokacin yajin aikin 'yan kwadago na baya

A kwanakin baya ne kungiyar kwadago ta Najeriya ta shiga yajin aiki na gargadi, bayanda aka kasa cimma daidaito tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayyar kasar bisa karin albashi.

Kungiyar kwadagon dai na son samun naira dubu goma sha takwas ne a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata a kasar. To amma yajin aikin bai kawo biyan bukata.

Ma'aikta dai sun sha yin irin wannan yajin aiki domin neman karin albashi, sai dai kuma watanni ko 'yan shekaru bayan karin albashin sai kaga an koma jiya iyau saboda wasu dalilai da dama.

Shin me ya sa har yanzu gwamnatin ta kasa aiwatar da sabon tsarin albashin? Ko ya dace har sai ma'aikatan sun yi yajin aikin, kafin su gani a kasa?

To domin tattaunawa a kan wannan batu, mun gayyato baki wadanda suka hada Comrade Danjuma Papakunene, shugaban bangaren mawallafa a kungiyar kwadago ta Nijeriya.

Sai kuma Malam Sani Yau Babura, mai sharhi kan harkokin yau da kullum, kuma tsohon shugaban yankin arewa maso yammacin Najeriya na kungiyar dillalan mai ta kasa, wato IPMAN.

Akwai kuma Senata Hassan Muhammad Nasiha, mataimakin shugaban kwamitin kwadago da samar da ayyukanyi a majalisar dattawan Najeriya. Sai kuma Malam Badamasi Muhammad Kasuwar Yanya, wani dan kasuwa a birnin Abuja.