Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Matakin farko bayan samun ciki

Image caption Mata masu juna biyu suna jiran ganin likita

Masana a harkar kiwon lafiya dai sun kasa ciki da mace ke dauka zuwa kashi uku, wato watanni uku na farko shine mataki na farko, sai watanni uku na tsakiya sannan kuma watanni uku na karshe, wato watanni tara ke nan.

To Baya ga hanyoyi da gwaji da mace kan iya bi don gano cewa tana da juna biyu, kamar yadda watakila kukaji a shirinmu da ya gabata wasu hanyoyin kuma da mace ke gane cewa ta samu juna biyu sun hada da rashin ganin al'ada, kasala, zub da yawu kwadayi da sauransu.

Kuma daga wannan lokacin ne kuma mace ta shiga mataki na farko na ciki da masana a fannin kiwon lafiya ke cewa first trimester a turance. Haka kuma daya daga cikin abubuwan da macen da samu juna biyu ke fuskanta a wannan lokaci, wanda kuma yafi janyo hankalin mutane ga halin da take ciki shi ne laulayi.

Kuma wannan matakin farko na ciki na da mayukar muhimmancin gaske a cewar masana wajen wanzuwar abinda Allah ya albarkaci mace da shi. Domin a wannan lokacin ne ake dukkan halitar dan adam a cikin mahaifiyarsa.

A wannan shirin za mu fara ne da bakuwarmu ta musamman wato mace mai juna biyu da cikinta bai wuce watanni uku ba. Domin mu ji irin yadda take tafi da rayuwarta na yau da kullum a cikin halin laulayin ciki da kuma abubuwan da ta kanyi don ganin ta rage kaifin laulayin da take fuskanta. Sannan daga bisani kuma muji mai likita za ta fada game da hakan.

Shirin haifi kiyaye kenan na wannan mako. Sai ayi sauraro lafiya