Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalolin tsaro a lokutan zabe a Najeriya

Image caption An dade ana samun tashin hankali a lokutan zabe a Najeriya

A yayin da zabukan Najeriya ke karatowa, wani batu dake haddasa fargaba a zukatan yawancin 'yan kasar shi ne matsalar tsaro a lokutan zabe.

Wani abin damuwa kuma shi ne yadda hukumomin tsaro suka kama makamai a gabar ruwan Legas, wanda wasu ke ganin ba zai rasa nasaba da yadda wasu ke daukar zabukan na badi ba, na ko a mutu ko ayi rai.

To ko wadanne dalilai ne ke haddasa irin wadannan rikice-rikicen siyasar?

Wadanne matakan rigakafi kuma ya kamata a dauka, domin tabbatar da cewa an gudanar da zabubukan na badi a Najeriya, cikin kwanciyar hankali?

To baya ga masu sauraron da ke kan waya, mun kuma gayyato baki na musamman, domin tattaunawa a kan wadannan batutuwan:

Injiniya Buba Galadima na jam'iyyar CPC da Dr Danladi Abdullahi Sankara, Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, mai kula da shiyyar arewa maso Yammacin Najeriya.

Akwai kuma Mr Nick Dazan, Mukaddashin jami'in hulda da jama'a na INEC, a Abuja. Sai kuma Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano Tambari Yabo Mohammed.