Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Karuwar matsalar cin hanci da rashawa

Image caption Bincike ya nuna cewa matsalar cin hanci na kan gaba a cikin abubuwan da ke damun jama'a a duniya

Batun cin hanci da rashawa batu ne da ya yi kamari a kasashe da dama na duniya, wanda kuma ke yin illa ga yadda ake gudanar da ayyukan al'umma.

Ana zargin manyan jami'an gwamnati da hada baki da kamfanoni, ko bankuna domin sace dukiyar da aka ware domin raya kasa.

Alal misali, a wani jawabi da ya gabatar a gaban majalisar dokoki ta Amruka, tsohon shugaban hukumar yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa abin da aka sace a Najeriya daga 1960 zuwa 1999 ya kai dalar Amruka biliyan 440.

Kuma a cewarsa, yawan wadannan kudade, sun haura kudaden da aka kashe a gagarumin shirin gina kasashen Turai bayan yakin duniya na biyu har sau shida.

To ko yaya lamarin yake a kasashe na Afrika Kamar Najeriya da Nijer da Ghana da Kamaru, sannan ta yaya za a warware tufkar zaren, wannan shi ne abin da zamu tattauna a filin ra'ayi riga.

To domin tattauna wannan batu mun gayyato baki da dama, wadanda suka hada da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, da Hon Rabe Nasir, shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa a majalisar wakilai ta Nijeriya.

Akwai kuma Malam Mamman Wada, sakataren kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashawa a Jamhuriyar Niger, sai kuma Malam Abubakar Othman, mataimaki na musamman ga shugabar hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.