Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rufe makarantu domin rijistar zabe

Image caption An dade ana sukar mahukunta kan tabarbarewar ilimi a Najeriya

Matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka na rufe makarantun Firamare da na Sakandire domin gudanar da rijistar masu zabe ya ja hankalin jama'a sosai a kasar, inda iyaye da dama suka nuna rashin gamsuwar su da matakin.

Hakazalika masu sharhi kan al'amuran yau da kullum suma sun soki wannan batu inda suka ce gwamnati ta baiwa siyasa muhimmanci a kan ilmi.

Wasu ma suna ganin wannan mataki 'ya'yan talakawa zai fi shafa domin a makarantun gwamnati za a fi yin wannan rijista, wadanda kuma 'ya'yan talakawa ne ke halarta.

Sai dai a nata bangaren gwamnati da hukumar zabe sun ce an dau wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro da gudanar da wannan rijista cikin tsanaki.

To domin shiga cikin wannan shiri mun gayyato baki da dama wadanda suka hada Ministar ilmi ta Nijeriya Farfesa Ruqayya Rufa'i, da Mr Nick Dazang mataimakin darektan hulda da jama'a a hukumar zabe ta Nijeriya.

Akwai kuma Dr Aliyu Tilde mai yin sharhi kan al'amuran yau da kullum a Nijeriyar. Sai masu saurare dake kan layi wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu.