Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalolin aikin rajistar masu zabe a Najeriya

A Najeriya, kusan mako guda kenan da fara aikin rajistar masu zabe, a daya daga cikin matakan da ake dauka na shirya wa zaben watan Aprilu.

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ce tana fatan yi wa mutane kimanin miliyan saba'in rajistar zaben.

To sai dai fara aikin rajistar ke da wuya aka yi ta korafe korafe da dama dangane da irin matsalolin da ake cin karo da su.

Domin tattaunawa kan rajistar masu zaben a Najeriya mun gayyato wasu baki da suka hada da, kwamishinan hukumar zabe na kasa mai kula da jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Danyaya, da Dr Danladi Sankara, mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa reshen arewa maso yammacin Najeriya, da Alhaji Faruk Adamu Aliyu, na jam'iyyar CPC a jihar Jigawa, akwai kuma Malam Awwalu Sadisu Baba, daga jami'ar Portsmouth dake nan Ingila, wanda masanin harkar sadarwa ce da ta shafi na'ura mai kwakwalwa. A yi sauraro lafiya.