Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dubban 'yan kasar Masar sun fita kan tituna suna murna

Shugaba Hosni Mubarak na Masar ya yi murabus, bayan da masu zanga-zanga suka matsa masa lamba.

Mataimakin shugaban kasa Umar suleoman ne ya bada sanarwar murabis din shugaban.

Dubban 'yan kasar Masar sun fita kan titunan a birnin Alkahira, suna murnar abin da suka dade suna nema.

Ita dai wannan zanga-zanga ta kin jin gwamnati ta samo asali ne bayan irinta da aka yi a kasar Tunisia, wadda ta tilastawa shugaba Zine al Abidin bin Ali ranta a na kare.