Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Sauye-sauyen sunayen 'yan takara a Najeriya

Image caption Sunayen sun haifar da cece-kuce a sassa da dama na kasar

Sunayen da hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya ta wallafa na wadanda zasu yi takara a zabe mai zuwa ya jawo cece-cece ku ce a kasar.

Bugu da kari hukumar zaben ta janye sunayen 'yan takarar wasu jam'iyyu a jihohi kamar Enugu da Oyo.

Shin me hakan zai iya haifarwa ga zabe mai zuwa, sannan ta yaya za a magance korafin da ya biyo bayan wallafa wadannan sunaye.

Wannan shi ne batun da zamu tattauna a filin ra'ayi riga na wannan makon.

To domin tattauna wannan batu, mun gayyato baki da dama, wadanda suka hada da: Malam Muhammad Haruna, wani fitaccen dan jarida kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, akwai kuma Barrister Yahaya Mahmud, wani lauya mai zaman kansa a Kaduna.

Sai kuma Mr Nick Dazang, mataimakin darektan hulda da jama'a a hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Daga bangaren 'yan siyasa kuma akwai: Honourable Musa Sarkin Adar, shugaban kwamiti mai kula da sauye-sauyen zabe a Majalisar wakilan Najeriya. Sannan muna tare da Alhaji Buba Galadima, sakataren jam'iyyar adawan CPC, Da kuma Parfesa Rufa'i Ahmed Alkali, kakakin jam'iyyar PDP mai mulki.