Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Dokar 'yancin yara a Nijar da Najeriya

Image caption Wannan doka dai ta dade tana shan suka daga kungiyoyin musulmi

Batun aiki da dokar mata da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ya janyo korafe-korafe daga kasashe irin su Nijeriya da Nijar inda ake da Musulmi masu dimbin yawa.

Wasu dokokin mata da kananan yara da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen duniya su runguma domin kyautata daidaiton 'yanci da ingancin rayuwa.

Wadanda suka hada da hana sanya yara aikin karfi da hana dukansu da kuma hana auren budurwar da ba ta kai shekaru 18 ba.

Sai dai hakan na haddasa cece - kuce a wasu kasashen, alal misali a Jamhuriyar Nijar - kwanan nan har wani gangami aka yi na nuna kyama a kan wadannan dokoki.

A Najeriya ma wadannan dokoki ba su samu amincewar galibin Jihohin Arewacin kasar ba.

To shi ma ya kamata a amince da wadannan dokoki, ko kuma yaya? Abinda muka tattauna akai kenan a filin mu na Ra'ayi Riga a wannan makon!

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato baki da kuma wasu daga cikinku ku masu saurarenmu.

Daga cikin bakin namu akwai : Sheikh Muktar Khalid Djibo, daya daga cikin wadanda aka tsara wadannan dokoki da su a Nijar,

Da Ustaz Isa Isma'il, daya daga cikin shugabannin kungiyar addinin Islama ta ACOE, masu adawa da shirin dokar.

Daga Nijeriya kuma akwai Ustaz Hussaini Zakariya, wani fitaccen malami a Abuja.