Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zabe mai inganci a Najeriya

A farkon makon nan ne mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka, Maria Otero ta kai ziyara Nijeriya, inda ta nuna cewa matsayin Amurka da Birtaniya shi ne cewar wajibi ne a wannan karon Nijeriya ta gudanar da zabe na gaskiya da adalci a zaben watan Aprilu mai zuwa. Ta ce ta haka ne kawai za a rika daukar Nijeriyar da kima a matsayin jagora a nahiyar Afrika, kuma hakan zai share ma ta fagen zama mai fada aji a duniya.

Amurka da Birtaniya sun ce zasu dauki matakan wayar da kan masu zabe a Nijeriyar, domin su fahimci hakkokinsu. Kasashen biyu sun kuma baiwa

Nijeriyar gudunmawar dala miliyan 35 , sama da naira biliyan biyar, domin gudanar da ayukan zaben. Shin ko irin wadannan kasashe da kungiyoyi na duniya zasu iya yin tasiri wajen gudanar da zabe mai tsabta a Nijeriya?

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato;

Dr Aliyu Idi Hong, minista a ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya, Dr Kole Shettima, Darakta a Ofishin Gidauniyar McAuthur,mai bayar da gudumawar kan fannonin raya kasa da kyauatata mulkin demokuradiya, da Alhaji Ibrahim Biu, Daraktan sashen Ilmantar da masu zabe na hukumar zabe ta kasa a Nijeriya, wadanda duk suke dakinmu na watsa shirye shirye dake Abuja, akwai kuma Dr Usman Bugaje, dan takarar gwamna na jam'iyyar ACN a jihar Katsina , baya ga ku masu saurare.