Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Hada baki da jami'an tsaro wajen magudi

Image caption Jami'an tsaro sun sha alwashin tabbatar da an yi zabe cikin adalci

A lokutan baya, an sha zargin jami'an tsaro da hannu a magudin da ake tafkawa a lokacin zabe a Najeriya.

Zargin dai kan kama daga na taimakawa wajen aikata magudin zaben ya zuwa taimakawa wajen tsorata masu jefa kuri'a da kuma satar akwatunan zabe.

Sai dai Jami'an tsaron suna musanta wannan zargi.

Yanzu haka dai wannan batu na dada janyo muhawara tsakanin 'yan kasar yayin da ake shirin soma gudanar da zabuka a kasar.

Wasu dai na ganin a wannan karon ma ba za ta canza zani ba, amma wasu kuma gani suke za a dan samu ingantuwar lamura.

Domin tattaunawa kan wannan batu, mun gayyato CP Suleiman Abba, tsohon Kwamishinan 'yansanda na Jihar Rivers, da yanzu aka tura Lagos.

Da Ambasada Sule Buba - Shugaban yakin neman zaben Gwamna Patrick Ibrahim Yakowa na Jihar Kaduna na PDP da Ibrahim Moddibo, kakakin yakin neman zaben dan takarar Shugaban kasa na Jama'iyar ACN, Malam Nuhu Ribadu.

Da kuma Malam Auwal Rafsanjani ...na cibiyar kyautata ayyukan majalisa a Najeriya ta Civil Society Legislative Advocacy Centre.

Akwai kuma masu saurarenmu dake kan waya.