Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: 'Yancin aikin jarida a kasashen Afrika

Image caption Yan jarida na da matukar mahimmanci a tsarin demokuradiyya

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe aanar 3 ga watan Mayun kowace shekara domin bikin ranar 'yancin 'yan jarida, taken bikin na bana shi ne muhimmancin 'yan jarida ga tsarin demokradiyya.

Ana amfani da wannan rana ce domin wayar da kan jama'a game da muhimmancin 'yancin 'yan jarida.

A kuma tunatar da gwamnatoci kan hakkin da ya rataya a wuyansu na mutunta 'yancin fadin albarkacin baki, kamar yadda yake a karkashin dokar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya.

Taken bikin na bana dai shi ne muhimmancin 'yancin 'yan jarida ga tsarin demokradiyya, imma jariri ko kuma wanda ya riku: Tare da taken "Shiru na kashe demokradiyya, to amma 'yancin 'yan jarida na farfado da shi".

Jama'a da dama sun yi amannar 'yan jarida na taka rawa wajen bankado irin ta'asa da cin hanci da rashawar da shugabanni ke yi tare da kawo sauyi a kasashen da gwamnatocinsu basa bin tsarin demokradiyya.

Matsalolin da 'yan jarida a kasashe masu tasowa ke fuskanta dai sun kama daga rashin kayan aiki da rashin horo ya zuwa talauci, abinda ake dangantawa da kai su fadawa cikin tarkon gwamnatoci ko masu fada a ji a kasashensu.

To ko a ganinku 'yan jarida a kasashe masu tasowa na da 'yancin gudanar da ayyukansu, kamar yadda ya kamata, wacce rawa ya kamata su taka wajen karfafa tsarin demokradiyya?

To domin tattaunawa kan wannan batu muna tare da: Alhaji SALIFOU LABO BOUSHE Ministan sadaswa na Nijar da Illa Kani, editan jaridar La GRIFFE kuma shugaban kungiyar dake sa ido kan ayyukan yan jarida UNUMED, a Jamhuriyar Nijar.

Da kuma Shuaibu Usman Leman, babban Sakataren kungiyar 'Yan Jarida ta Najeria (NUJ) da kuma Auwalu Salihu, Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Nigeria, NBC.