Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yawan hadura a kasashe masu tasowa

Image caption Wani hadarin mota a Najeriya

Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun ce, mutane miliyan daya da dubu dari uku ne ke mutuwa a kowace shekara a duniya, sakamakon haduran motoci, inda 50 ke jikkata.

Fiye da kashi tasa'in cikin dari na hadurran su na faruwa ne a kasashe masu tasowa inda kusan a kullu yaumin za ka samu labarin hadarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane.

Alal misali ko a ranar Juma'a sai da wani hadari ya afku a kauyen Kukar Awo da ke kusa da garin Potiskum a Jihar Yobe da ke Arewacin Najeriya. Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wannan hadari.

To Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce, idan ba a yi wani abu ba a kan irin wadannan hadarurruka ba, to kuwa yawan mace-macen mutane, zai kai miliyan daya da dubu dari tara, nan da shekara ta dubu biyu da ashirin.

To domin tattaunawa a kan dalilan da ke janyo hadurran motocin da kuma gano bakin zaren lamarin, mun gayyato bakin da suka hada da Alhaji Daiyyabu Garga, Sakatare Janar na kungiyar direbobin tankokin daukar mai na kasa a Najeriya.

Da Alhaji Ahmad Hassan Kogari (Kwamandan Hukumar kare hadurra ta kasa, reshen jahar Kano) da Alhaji Bako Umar, Shugaban kungiyar Direbobi ta kasa a Najeriya, NURTW reshen Jihar Kano ).

Da Alhassan Samba, Shugaban kungiyar direbobin motocin fasinja mai zurga-zurga tsakanin Accra zuwa - Aflao da kuma Lome da kuma tsakanin Accra zuwa Elubo kan iyaka da kasar Ivory Coast.

Akwai kuma Malam Maiga Djibo Ibrahim, shugaban kungiyar Peaceful Roads mai kula da kare hadurra akan hanyoyi a Nijar, da wasu daga cikin masu saurare.