Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar tsaro a Najeriya, ina mafita?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Jonathan ya yi alkawarin kawo karshen hare-haren

A Najeriya ana dada fuskantar kalubale wajen tabbatar da tsaro bayan harin bam din da aka kai ranar Alhamis, a hedkwatar 'yan sandan kasar a Abuja, wanda ya janyo hasarar rayuka da dukiya.

Tuni dai kungiyar nan ta Ahlus Sunna Lil-da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ta kai harin.

Sai dai shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce jami'an tsaron kasar na kokarin shawo kan hare-haren bama-bamai da ya kira na ta'addanci ne da ake ci gaba da kaiwa a kasar.

Editan BBC a Abuja Bashir Sa'ad Abdullahi, ya ce harin na ranar Alhamis shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren bama-bamai da ake kaiwa a kasar a 'yan watannin da suka gabata.

Duka shugaba Jonathan da kuma gwamnan jihar Borno inda kungiyar ta Boko Haram ta fi kai hare-hare, sun nemi kungiyar da ta zo a tattauna domin kawo karshen rikicin.

Sai dai kungiyar ta yi watsi da kiran na su.

Ita dai kungiyar na kira ne da a tabbatar da cikakken tsarin shari'ar musulunci a wasu jihohin Arewacin kasar.

To domin tattaunawa kan wannan batu na tsaro a Najeriya, mun gayyato bakin da suka hada da:

Kwamishinan 'yan sandan jahar Rivers, Suleiman Abba da Manjo Yahaya Shinko mai ritaya, mai nazari kan harkokin tsaro a Najeriya.

Sai kuma Alhaji Walid Jibril, dan kwamitin amintattun jam'iyyar PDP da kuma Dokta Usman Bugaje, dan jam'iyyar adawa ta ACN.