Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yiwuwar ambaliya a Najeriya da Nijar

Image caption Tuni dai aka fara samun ambaliyar ruwan a Najeriya

Hukumomin hasashe kan yanayi a kasashen Nijeriya da Nijer sun yi hasashen cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a kasashen biyu saboda ruwan saman da ake sa ran za a tafka a bana.

Idan dai hakan ta kasance to zai iya shafar al'amuran rayuwa jama'a.

Ganin cewa damina ta fara nisa, shin ko wanne irin mataki hukomomi ke dauka kan wannan hasashe, me ya kamata jama'a su yi domin kaucewa shiga hadarin ambaliyar ruwan?

Domin tattaunawa kan wannan batun, muna tare da Malam Nuhu Alhassan, mataimakin darakta kan tsare-tsare da bincike da kuma hasashe na hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya Nema,

Da Alhaji Abdullahi Abbas, kwamishinan muhalli na jihar Kano. Da Malam Salisu Auwal babban jami'i a hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya,

A Jamhuriyar Nijar kuma muna tare da Malam Idy Baraou, wakilinmu a Yamai wanda ya sha aiko da rahotanni lokacin da akai ambaliya a jamhuriyar Nijer.

Sai kuma masu saurare da ke kan layi wadanda zasu bayyana ra'ayoyinsu: