Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rashin tsabtace muhalli

Hakkin mallakar hoto water journalist africa
Image caption Rashin tsaftace muhalli na haddasa cututtuka da dama

Daruruwan jami'ai daga kasashe kimanin hamsin na Afrika ne suka halarci taron da aka gudanar a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, kan tsabtace muhalli.

An shirya taron ne da nufin farkar da Afirka, game da cinma muradun karni kan tsabta, nan da 2015.

Yanzu an ce kasashe hudu ne kawai a Afrika suke kan hanyar cinma muradun ganin an rage da kamar rabi, yawan mutanen da ke zaune cikin kazanta, nan da shekaru biyar masu zuwa.

Cutar gudawa, wadda asalinta rashin tsabta ne, tana sanadiyar mutuwar kananan yara miliyan guda a kowace shekara, wasu kuma fiye da hakan na kwantawa rashin lafiya dalilin hakan.

A wannan shirin, zamu so mu ji halin da kuke ciki game da tsabtar muhallin.

Sannan kuma zamu tattauna akan illolin rashin tsabta, da kuma matakan kariya.

Ayi sauraro lafiya.