Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tsadar abinci lokacin azumi

Hakkin mallakar hoto Getty

Yayinda ake shirin fara azumin watan Ramalana, wasu abubuwa da jama'a suka fi kuka da shi a lokacin azumin shi ne batun tsadar kayayyakin abinci da sauran na masarufi.

Shin wane shiri jama'a suke yi na tunkarar azumin na bana, kuma wadanne irin darussa ake koya a lokacin azumin?

Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna kan su a shirinmu na Ra'ayi Riga na yau. Baya ga ku masu sauraro dake kan layi, wasu daga cikin bakin da muka gayyato sun hada da Sheikh Ibrahim Khalil, wani malami a Kano, da Alhaji Kabiru Hali, shugaban kungiyar 'yan kasuwa na jihar Sokoto, da kuma Alhaji Sama'ila Hatim Mai'aya, shugaba 'yan kasuwa na Nijar.

A yi sauraro lafiya.