Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Batun wa'adin mulki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watan Mayun bana ne aka rantsar da Shugaban Goodluck Jonathan

Batun wa'adin mulki guda na fiye da shekaru hudu, ga shugaban kasa da kuma gwamnoni a Nijeriya, batu ne ya sake janyo kace-nace a 'yan kwanakin nan.

Tun bayan da wasu kafafen yada labarai suka tsegunta cewa shugaba Goodluck Jonathan na duba yuwuwar gabatar da shirin doka ga majalisar dokoki ta kasa, kan batun, a wani bangare na yi wa kundin tsarin mulki garambawul.

Wannan dai ba shi ne karon farko da batun ya taso ba, ko a zamanin gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo an yi ta ce-ce-ku-ce a kansa, daga bisani majalisar dattawa ta yi watsi da shi.

To wane alfanu ne ke tattare da wannan tsari na wa'adin mulki guda ga shugaban kasa ko gwamna, da wasu ke goyon bayan ganin an bullo da shi, menene kuma nakasunsa da wasu ke adawa shi?

Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna kansu a filinmu na ra'ayi Riga na yau.

To baya ga masu saurare da ke kan layin tarho, mun gayyato wasu baki da za mu ji ra'ayoyinsu a kan wannan batu, wadanda suka hada da Alhaji Tanko Yakasai, a Kano wani gogaggen dan siyasa a Najeriya da Alhaji Isa Tafida Mafindi, dan kwamitin amintattu na jama'iyar PDP na kasa.

Da kuma Malam Abubakar Kari na Jami'ar Abuja, can kuma a Katsina akwai Alhaji Ibrahim Masari shi ma wani dan siyasa.