Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Me ke janyo cin hanci da rashawar?

Cin hanci da rashawa na cigaba da yin kafar ungulu ga bunkasar kasashe, duk da makudan kudaden da gwamnatoci ke kashewa wajen neman dakile matsalar, da kuma kokarin da kungiyoyi masu zaman kansu ke yi wajen kawo tasu gudunmawar.

A cikin rahoton da ta fitar kasa da shekara guda kenan, kungiyar Transparency International, mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya, ta ce kusan kashi uku cikin hudu na kasashe 178 da ta gudanar da bincike a kansu, sun kasa samun maki 5 bisa goma.

Kasar da ta zo ta daya wajen rashin cin hancin ita ce Denmark, sannan New Zealand na biye mata.

Birtaniya tana a matsayi na ashirin, Amruka kuma na matsayi na ashirin da biyu.

A nahiyar Afrika kuwa, Ghana tana matsayi na sittin da biyu (62), Nijar tana matsayi na 123, yayin da Najeriya ta zo ta 134, Kamaru kuma kuma take matsayi na 146.

Babbar tambaya ita ce: me ke janyo cin hanci da rashawar? Sannan ina mafita?

Bakin da muka gayyato a shirin - baya ga masu sauraro da ke kan layi - sun hada da:

1. Malam Mahamane Hamisu Mumuni, mataimakin shugaban hukumar koli ta yaki da cin hanci da rashawa a Nijar

2. Dokta Abubakar Othman, mashawarci ga shugabar hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

3. Mallam Abba Anwar, jami'in kungiyar Transparency International mai kula da shiyyar arewa maso yammacin Najeriya

A yi sauri sauraro lafiya.