Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Guguwar sauyi a kasar Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tun watan Fabreru ake fafatawa tsakanin 'yan tawaye da Kanal Gaddafi

Tun a watan Fabrairu ne guguwar sauyin dake kadawa a wasu kasashen Larabawa, ta shiga kasar Libya, kuma daga lokacin ne ake ta artabu tsakanin dakarun 'yan tawaye da kuma dakarun Kanar Gaddafi.

Yanzu haka, 'yan tawayen na Libya sun kame galibin birnin Tripoli da sauran sassan kasar, amma har yanzu akwai yankuna da dama, inda sojojin da ke biyaya ga Kanar Gaddafi su ka ja daga.

Daya daga cikin irin wadannan yankuna, shi ne birnin Sirte, mahaifar Kanar Gaddafin. Duk da cewa har yanzu Kungiyar Tarayyar Afrika ba ta amince da gwamnatin 'yan tawaye ba, to amma kasashen Afrika da dama, ciki har da Najeria da kuma Nijar, sun fito sun nuna goyon bayansu ga 'yan tawayen.

Tambayar da ake yi yanzu haka ita ce: Wane irin tasiri ne wannan sauyin da ake samu a kasar ta Libyar zai yi a wannan yanki, da ma Afrika baki daya?

Mun tattauna da wani mazaunin kasar ta Libya domin jin halin da ake ciki. Baya ga shi kuma muna tare da:

Ambasada Isuhu Bashar, tsohon jakadan Nijar a Libiya; da kuma Sherrif Muhammad Zaydan Waddani, wakilin 'yan tawayen Libyar a Nijar, wadanda dukansu ke birnin Yamai.

Akwai kuma Ambasada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya a Sudan, kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum.

Sai kuma a Accra Ghana, muna tare da Sheikh Usman Bari, tsohon jami'in jakadancin kasar ta Ghana, kuma masanin tarihi.