Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zaben shugaban kasa a Kamaru

Hakkin mallakar hoto Paul Biya
Image caption Tun shekarar 1982 shugaba Paul Biya ya ke mulki a kasar

Ranar Lahadi ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Kamaru, wanda zai hada 'yan takara fiye da ashirin, ciki har da shugaba mai ci a yanzu, Paul Biya.

'Yan Kamaru fiye da miliyan bakwai ne suka yi rajistar shiga zaben, daga cikin 'yan kasar su kimanin miliyan 19 da rabi.

An tanadi rumfunan zabe kimanin dubu ashirin da hudu.

A cikin kwanaki goma sha biyar ne ya kamata a bayyana sakamakon zaben, mai zagaye guda kawai.

To ko kun gamsu da shirye shiryen zaben? Me kuma ya kamata masu jefa kuri'a su yi la'akari da shi idan sun zo zaben?

Kadan kenan daga cikin irin abubuwan da zamu tattauna akai, a filin Ra'ayi Rigar na wannan makon.

To baya ga masu sauraron da ke kan layi suna jiran su bayyana ra'ayoyinsu a kan zaben, mun kuma gayyato bakin da suka hada da:

Ousman Alhadji, mai sharhi kan al'amurran yau da kullum a Yaounde da Alhadji Amadou Tidjani Dan Ba, mataimakin shugaban jam'iyyar RDPC mai mulki, a unguwannin Aoudi/Tapare, a garin Ngaoundere.

Mouhamadou Nasiru Bagaya, shugaban jam'iyyar UNDP mai kawance da RDPC, reshen Yaounde ta biyu, da Alhadji Oumarou Garba, mashawarcin jam'iyyar adawa ta SDF, a Bamenda.

Sai kuma Sani Alhadji Yaro Matan Haoussa, shugaban kungiyar kare hakkin jama'a da demokradiyya a Yaounde, kuma mai sa ido akan zaben na ranar Lahadi.