Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Janye tallafin mai a Najeriya

Hakkin mallakar hoto google
Image caption An dade ana takaddama kan wannan batun a Najeriya

A yanzu haka dai gwamnatin Najeriya ta niki garin janye tallafin kudaden da take bayarwa ga bangaren man fetur a kasar. Amma Majalisar Dattawa ta ce a yi bincike tukunna.

A cewar gwamnatin, tana so ne ta yi amfani da kudaden wajen yin ayyukan raya kasa.

To amma a ganin masu adawa da matakin, janye tallafin zai sa talaka ya kara shiga cikin halin o-ni-'yasu, kuma kudaden za su salwanta hakanan.

A yayin da ake ci gaba da ja-in-ja akan batun, majalisar dattawan Najeriyar ta bada umurnin a gudanar da bincike, akan yadda ake kashe kudaden tallafin, kamin ta san matakin da za ta dauka.

To a filin na Ra'ayi Riga, baya ga masu sauraron da ke kan waya suna jiran su tofa albarkacin bakinsu, akwai kuma bakin da muka gayyato, wadanda suka hada da:

Alhaji Isa Tafida Mafindi, dan kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP mai mulki. Comrade Abdulwahid Umar, Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC.

Da Sanata Ahmed Lawan, dan majalisar dattawa da Farfesa Murtala Sagagi, na sashen nazarin ilimin tattalin arziki, a jami'ar Bayero da ke Kano.