Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Makomar Libya bayan Kanal Gaddafi

Image caption Akwai babban kalubale a gaban jami'an gwamnatin riko ta NTC

Bayan da dakarun 'yan tawayen Libya suka kashe tsohon shugaban kasar, Kanar Mu'ammar Gaddafi, a kusa da birnin Sirte mahaifarsa. Ko meye makomar kasar?

Shi dai Kanar Gaddafin ana yi masa kallon mazari, ba a san gabanka ba, ba kawai a tsakanin kasashen yammacin duniya ba, har ma a kasashen Larabawa ba, da ma sauran kasashen duniya.

Wasu na kallon kisan nasa a matsayin karshen wani babi, bayan da ya shafe sama da shekaru arba'in yana mulki.

Yayin da wasu kasashen yammacin duniya ke yi masa kallon mai mara baya ga ayyukan ta'addanci, wasu kuma na kallonsa ne a matsayin gwarzo, wanda ke kallon kasashen yammacin duniya, yana ce masu cas, a duk lokacin da suka ce masa kule.

To yanzu da yake an kashe Kanar Gaddafin, ko hakan zai kawo karshen zub da jini a kasar ta Libya, tun bayan boren da aka fara cikin watan Fabrairu?

Me zai kasance makomar kasar, kuma wane irin kalubale ke gaban sabbin mahukuntanta?. Wasu kenan daga cikin abubuwan da Filin Ra'ayi Riga na wannan makon zai tattauna kansu.

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato; Ambasada Isuhu Bashar, tsohon jakadan Nijar a Libya da Ambasada Sulaiman Dahiru, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Nijeriya. Da kuma Sheikh Usman Bari, shi ma wani tsohon jami'in jakadancin kasar Ghana, kuma masani kan siyasar yankin gabas ta tsakiya.