Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: "Rashin aikin yi ga matasa ya ta'azzara"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu matasa na zanga-zangar rashin aikin yi a Morocco

A wani rohoto da ta fitar a kan matsalar rashin aikin yi a duniya, Hukumar Kwadago ta Duniya, ILO ta ce ta gano cewa yawan masu zaman kashe wando da kuma wadanda ke ayyukan da ba sa samar masu da wani abun kirki, ya kai miliyan 75 a duniya.

Wannan lamari a cewar hukumar zai iya haifar da mummunan sakamako a gaba, saboda matasa za su dawo daga rakiyar tsarin siyasar kasashensu, kuma suna ina yin bore.

Rahoton, wanda hukumar ta fitar a karshen watan Oktoba, ya zo ne watanni, bayan boren da ya kai ga hambarad da wasu shugabannin Africa.

Kungiyar ta ILO ta gudanar da binciken ta ne a kasashe 119 da suka hada da na Afrika.

Ko yaya matsalar rashin aikin yi take a tsakanin matasa a yankunan ku? Ta yaya kuma za'a magance wannan matsala?

To domin tattaunawa akan wannan batu, mun gayyato wasu baki da suka hada da :

Malam Mohammed Abubakar, Shugaban hukumar samar da ayyukan yi ta kasa a Nigeria, ta NDE, da Farfesa Murtala Sagagi Masanin tattalin arzikin kasa a Jami'ar Bayero da ke Kano.

Ahmed Adamu babban mai tsawatarwa na majalisar matasa ta Nigeria da kuma Boubakar Shalare tsohon shugaban kungiyar masu neman aiki a jamhuriyyar Nijar, wanda a halin yanzu yake da komfanin sa na kansa.