Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Ta yaya 'yan Nijar za su amfana da arzikin mai?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wata Matatar Mai

A ranar Litinin ake kaddamar da matatar man fetur ta farko a Jamhuriyar Nijar a garin Dan-Baki da ke jihar Damagaram.

Matatar Man, mai suna SORAZ, za ta samar da gangar mai dubu 20 a kowacce rana, don amfanin cikin gida da kuma sayarwa kasuwannin kasashen waje.

Tun daga lokacin ne 'yan Nijar suka shiga nuna kyakyawan fata na cin gajiyar wannan arziki da Allah ya horewa kasar.

To sai dai sabon farashin man da gwamnati ta tsaida a kwanan nan, yana neman sawa murna ta koma ciki.

Alkalumman gwamnatin Nijar din sun nuna cewa, yawan albarkatun man da aka gano a kasar ya zuwa yanzu, ya kai ganga miliyan dari 4 da 80.

To ko ta yaya wannan arzikin mai zai canza rayuwar talakawan kasar, kuma me ya kamata a yi don a tabbatar cewa duka 'yan kasar ta Nijar sun amfana da shi?

Kadan kenan daga cikin irin abubuwan da shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan mako ya mayar da hankali a kai.