Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar karancin abinci a wasu sassan Afrika

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Kungiyar Oxfam ta ce za a fuskanci karancin abinci a wasu sassan Afrika

A farkon makon nan ne kungiyar agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar karancin abinci a wasu kasashen Afrika da suka hada da Nijar da Chadi da Mali da Burkina Faso da ma wasu jihohi a arewacin Najeria.

Rohoton ya ce matsalar nada alaka ne da karancin ruwan sama da kuma sauyin yanayi.

Ko a kwanakin baya ma, Kungiyar Tarayyar Turai ma ta yi irin wannan gargadin.

A cewar kungiyar ta OXFAM, a wasu kasashen tuni har farashin hatsi ya yi sama da kamar kashi 40 cikin dari.

A bara ma an yi fama da karancin abinci, kuma yanzu haka ma ana fama da matsalar a wasu kasashen Afrika.

To wannan batu ne dai za mu tattauna a kai a filin mu na Ra'ayi Riga.

Kuma domin tattaunawa kan wannan matsala da kuma yadda za a shawo kanta, mun gayyato baki da suka hada:

Mista Daniel Daudu, Shugaban shirin wadata kasa da abinci a Najeria, da Dr. Mohammed Jabbi Kilgori, Kwamishinan aikin gona na jihar Sokoto a Arewacin Najeriya.

Akwai Dr Husaini Abdu, Shugaban kungiyar agaji ta Actionaid a Najeriya, wadda ke aiki kafada da kafada da kungiyar Oxfam da ta fitar da rohoton.

Sai kuma Malam Mahamman Sani Abdu, babban darekta a ma'aikatun gidan gona a ma'aikatar ayyukan noma.

Sai kuma wasu daga cikin masu sauraronmu: