Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Kalubalen da ke gaban shekara ta 2012

Image caption An dai fuskanci kalubale da dama a shekarar 2011

Muhimman abubuwa da dama ne dai suka faru a wannan shekara mai karewa: An yi zaben shugaban kasa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

A cikinta ne kuma Sudan ta kudu ta samu 'yanci. Sai dai kuma shekarar ta zo da kalubale.

Baya ga tsadar rayuwa a wurare da dama, rashin tsaro ya kasance wata babbar matsala da ke ci wa jama'a da mahukunta tuwo a kwarya a kasashe kamar su Najeriya.

Menene hasashen ku akan matsalolin da kuke jin za a iya fuskanta a shekara mai zuwa, kuma ta yaya za a bullo masu, kana kuma mene ne fatanku?

Wasu kenan daga cikin irin abubuwan da muka tattauna kan su a filin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

Za mu ji ra'ayoyinku kai tsaye ta waya, akan wannan batu, baya ga wadanda za su bayyana ra'ayoyin nasu ta facebook ko ta email da wayar salula.

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato Barrista Ahmed Gulak Mai bai wa shugaba Goodluck na Najeriya shawara ta fuskar siyasa.

Akwai kuma Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja kuma mai sharhi akan al'amurran yau da kullum.

A Nijar kuma za mu ji daga Moussa Tchangari wani mai sharhi akan al'amurran yau da kullum.

Akwa kuma Kalla Moutari Mataimakin Babban Sakataren fadar shugaban kasar Nijar, kuma muna tare da su ne ta waya.