Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Bukin kirsimatin shekarar 2011

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana bikin Kirsimati a sassa da dama na duniya

A ranar Lahadi ce mabiya addinin Kirista a ko'ina cikin duniya ke bukukuwan Kirsimati na bana. Ana bukukuwan ne domin tunawa da ranar Haihuwar Yesu Kiristi.

A kasashen Afrika irin su Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Ghana, a kan gudanar da bukukuwan ne ta hanyar shirya abinci iri-iri.

Da sanya sabbin tufafi a tafi mujami'u domin yin addu'o'i, da kai ziyara ga gidajen 'yan uwa da abokan arziki.

To ko ya kirsimatin ta bana ta zo wa jama'a, wadanne irin abubuwa ya kamata a rika yi a lokacin bukukuwan kirsimati, kuma wadanne darussa ya kamata a koya a daidai irin wannan lokaci?

Wasu kenan daga cikin irin abubuwan da za mu tattauna a kansu a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

Domin gabatar da shirin mun gayyato baki daban-daban cikinsu harda Rev. Ibrahim Usman a Katsina, Najeriya, sai kuma ku masu sauraro dake kan layi.