Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga sun fita kan tituna a sassan Najeriya daban-daban

Tun daga ranar Litinin ne aka fara yajin aikin gama-gari, da kuma zanga-zanga a duk fadin Najeriya domin adawa da matakin gwamnati na janye tallafin man fetur.

Hakan ya biyo bayan kiran da babbar kungiyar kwadago ta kasar, NLC ta yi ne na a kaurace ma wuraren aiki, a kuma fita kan tituna domin zanga-zanga.

Shugaba Goodluck Jonathan ya bada sanarwar janye tallafin ne a ranar 1 ga watan Janairun 2012, abinda ya sanya farashin mai da na sufuri suka ninka.

'Yan kasar da dama sun nun rashin amincewarsu da wannan matakin suna masu cewa tallafin man shi ne kawai abinda suke amfana daga dinbin arzikin man da Allah ya horewar kasar.

Rahotanni daga sassan Najeriya da dama sun nuna cewar an samu barkewar tashin hankali a wasu wuraren, sakamakon arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, lamarin da ya haddasa asarar rayuka.

Har yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin shugabannin kwadago da kuma jami'an gwamnati, sai dai kawo yanzu babu wata matsaya da aka cimma.

Shugabannin kungiyoyin kwdago sun ce ba za a gudanar da yajin aiki da zanga-zanga a ranar Asabar da kuma Lahadi ba.

Wannan dai na nufin jama'a za su yi zirga-zirga da kuma sauran al'amura na yau da kullum, cikin harda zirga-zirgar jiragen sama.

Ranar Lahadi mai zuwa ne kungiyar ma'aikatan mai ta kasa ta yi kurarin za ta fara hana fitar da danyan mai daga Najeriyar.

Daga cikin wadanda muka gayyato domin tattaunawa a filin namu na Ra'ayi Riga akwai, Dr Bukar Tijjani, Minista a ma'aikatar kudi ta Nijeriya, da Hon Aminu Nasiru Fagge, dan majalisar wakilan Najeriya.

Akwai kuma a bangaren kungiyar kwadago Malam Kiri Muhammed, mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, sai kuma ku masu sauraro da ke kan layi