Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shirin auren Zaurawa 1000 a Kano

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Rahotanni sun ce akwai dubban zaurawa a jihar ta Kano

Hukumar Hizba a Kano ta bullo da wani shiri, wanda ta ce zai taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro da rashin tarbiyyar da ake fama da su a jihar.

A cewar Hizbar, wani binciken da ta yi ya gano cewa, kashi saba'in da biyar na matsalolin karuwanci da shaye-shaye, ana samun su ne a tsakankanin zawarawa da marayu, da kuma yaran da iyayensu basa tare.

Hukumar ta Hizba ta ce, yanzu haka akwai zawarawa sama da miliyan daya a jihar ta Kano, kuma ta kuduri aniyar aurar da su sannu a hankali.

Za kuma ta fara ne da aurar da zawarawa dubu daya nan ba da jimawa ba, a zagayen farko na shirin.

Hukumar ta aikewa majalisar dokokin jihar wani kudirin doka mai kunshe da ka'aidojin shirin, don tabbatar da cewa auren zawarawan ya yi karko.

Ra'ayin jama'a dai ya sha bambam dangane da wannan aniya ta Hizbar ... don haka ne ma muka so mu tattauna akan shirin, a filin namu na wannan makon.

Kuma bakin da muka gayyato sun hada da: Malam Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban hukumar Hizba ta Jihar Kanon da Hajiya Altine Abdullahi, shugabar kungiyar zawarawa ta Jihar Kanon.

Akwai kuma Mal Muhammad Hadi Musa, Masani akan zamantakewar jama'a, kuma daraktan cibiyar bincike akan al'amurran musulunci ta kasa da kasa, a Jami'ar Bayero da ke Kanon.

Za mu kuma ji ra'ayoyin ku masu sauraro, ko dai kai tsaye ta waya, ko kuma mu karanto wadanda kuke aiko mana a rubuce.