Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Taron kasashen duniya kan Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Somalia na fama da matsaloli iri daban-daban da suka hada da karancin abinci

Shekaru sama da ashirin kenan da ake ta fama da rikici a Somalia, tun bayan hambarar da gwamnatin Siad Barre a 1991, wadda ake zargi da fifita haularsa ta Darood.

Tun daga wannan lokacin ne kuma haulolin Somaliyar suka shiga zaman 'yan marina, kasar ta kasance bata da gwamnatin tsakiya, illa gwamnatocin rikon kwaryar da ba sa kai labari, saboda rarrabuwar kawuna.

An sami kungiyoyin tawaye da dama a Somaliyar - a yanzu mafi girma ita ce Al-Shabaab mai fafatawa da gwamnatin wucin-gadin Somaliyar, wadda kuma a kwanan nan ta kulla kawance da kungiyar Al Qaeda.

Gwamnatin Burtaniya bata gayyaci Al Shabaab din ba a taron London da aka shirya kan makomar Somaliyar.

Can kuma a gabar tekun Somaliyar, 'yan fashi a teku na ta cin karensu ba babbaka, yayin da suke kama jiragen ruwa don neman kudin fansa.

Sannan kusan mutane miliyan biyu da rabi na fama da yunwa a kasar, inda dubbai ke zaune a sansanonin gudun hijira, a kasashe makwabta.

Bakin da muka gayyato a shirin sun hada da: Farfesa Djibo Hamani, malami a jami'ar Abdulmuninu Dioffo dake birnin Yamai da Dr. Abubakar Sadik, Malami a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Sai kuma Sheikh Usman Bari, tsohon jami'in diplomasiyya, kuma masanin siyasar Afirka da yankin gabas ta tsakiya, wanda ke birnin Accra an kasar Ghana.

Akwai kuma Alhaji Ahmed Gulak, mai ba shugaban Najeriya shawara ta fuskar siyasa, a ofishinmu na Abuja. Muna kuma tare da masu sauraro da yawa ta wayar tarho.