Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shiri na musamman kan cikar BBC shekaru 80

Image caption An gabatar da shirin ne a cikin wannan tantin na musamman

A wani bangare na shirye-shiryen da aka gudanar domin bikin cika shekaru 80 da kafa gidan rediyon BBC mai watsa shirye-shiryensa zuwa kasashen waje wato World Service a Turance.

An kafa wani tanti a tsakiyar Bush House inda sashin Turanci tare da sauran sassan BBC 16, suka gabatar da shirye-shirye daban-daban kuma kai tsaye daga wannan tanti.

Gidan rediyon BBCn ya kuma gayyato baki da daban-daban da suka hada da dalibai da tsaffin ma'aikata domin shiga a dama da su a shirye-shiryen.

Ana sa bangaren sashin Hausa na BBC ya gayyato Mr Barry Burgess tsohon editan BBC Hausa da kuma Sulaiman Ibrahim Katsina wanda yaga jiya-kuma yake ganin yau, domin gabatar da shiri na musamman.

Can a Abuja kuma akwai Saleh Aliyu Hadejia da kuma Umar Yusuf Karaye.

A cikin shirin wanda Aishatou Moussa ta jagoranta, an yi waiwaye adon tafiya kan rawar da BBCn ta taka a shekarun da ta shafe, da kuma yadda za a fusakanci gaba.

Wannan biki dai na zuwa ne a daidai lokacin da BBCn ke shirin barin Bush House, gidan ta shafe shekaru sama da 70 tana watsa shirye-shirye daga cikinsa.

A bana ne BBC za ta koma sabon kasaitaccen ofishinta na watsa labarai, Ma'aikatan World Service za su hadu da sauran takwarorinsu na BBC - da masu aiki kan shafukan internet da kuma talabijin - domin samar da ingantattun labaran duniya.