BBC navigation

Shiri na musamman kan cikar BBC shekaru 80

An sabunta: 29 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 19:36 GMT

Garmaho

Sashin Hausa na BBC ya gabatar da shiri na musamman domin bikin cikar gidan rediyon BBC mai watsa shirye-shiryensa zuwa kasashen waje shekaru 80 da kafuwa.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

BBC

An gabatar da shirin ne a cikin wannan tantin na musamman

A wani bangare na shirye-shiryen da aka gudanar domin bikin cika shekaru 80 da kafa gidan rediyon BBC mai watsa shirye-shiryensa zuwa kasashen waje wato World Service a Turance.

An kafa wani tanti a tsakiyar Bush House inda sashin Turanci tare da sauran sassan BBC 16, suka gabatar da shirye-shirye daban-daban kuma kai tsaye daga wannan tanti.

Gidan rediyon BBCn ya kuma gayyato baki da daban-daban da suka hada da dalibai da tsaffin ma'aikata domin shiga a dama da su a shirye-shiryen.

Ana sa bangaren sashin Hausa na BBC ya gayyato Mr Barry Burgess tsohon editan BBC Hausa da kuma Sulaiman Ibrahim Katsina wanda yaga jiya-kuma yake ganin yau, domin gabatar da shiri na musamman.

Can a Abuja kuma akwai Saleh Aliyu Hadejia da kuma Umar Yusuf Karaye.

A cikin shirin wanda Aishatou Moussa ta jagoranta, an yi waiwaye adon tafiya kan rawar da BBCn ta taka a shekarun da ta shafe, da kuma yadda za a fusakanci gaba.

Wannan biki dai na zuwa ne a daidai lokacin da BBCn ke shirin barin Bush House, gidan ta shafe shekaru sama da 70 tana watsa shirye-shirye daga cikinsa.

A bana ne BBC za ta koma sabon kasaitaccen ofishinta na watsa labarai, Ma'aikatan World Service za su hadu da sauran takwarorinsu na BBC - da masu aiki kan shafukan internet da kuma talabijin - domin samar da ingantattun labaran duniya.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.