Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yaya za a shawo kan rikicin kasar Syria?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An shafe shekara guda ana fama da rikici a ksar ta Syria

Shekara guda kenan da guguwar neman sauyi ta fara kadawa a kasar Syria inda yanzu haka 'yan adawa dauke da makamai ke kokarin kifar da gwamnatin Shugaba Bashar Assad. Ko yaya za a shawo kan matsalar?

Kazamin gumurzun da ake yi tsakanin 'yan adawa da sojojin gwamnatin Syriar dai ya haddasa dimbin asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyastawa cewa mutane akalla dubu bakwai da dari biyar ne suka rasa rayukansu, tun bayan da aka fara boren.

Boren wanda ya fara a birnin Deraa na kudancin kasar, ya bazu daga bisani zuwa sauran manyan biranen kasar da suka hada da Baniyas da Homs da kuma Hama, duk kuwa da matakan murkushe 'yan adawa da gwamnatin kasar ke dauka.

Wannan bore dai ya kasance kalubale mafi girma da mulkin gidansu Assad din suka fuskanta a shekaru 40 din da suka yi suna mulkin kasar.

Kasashen duniya dai suna ci gaba da yunkurinsu na kawo karshen zubar da jinin da ake yi a Syriar inda a kwanan baya kungiyar kasashen Larabawa ta aike da tawagar jami'an sa ido, amma ba tare da cimma wata nasara ba.

Wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ke goyon bayan wani shiri na kungiyar ta kasashen Larabawa game da yadda za a kawo karshen rikicin na Syriar ya ci karo da adawar Rasha da China, wadanda ke da kyakyawar dangantaka da Syriar.

Rashar dai ta ce kudurin zai iya share fagen daukar matakin soja a kan kasar ta Syria.

Yanzu haka kuma Majalisar Dinkin Duniyar ta nada manzo na musamman, watau tsohon babban magatakardarta Kofi Annan domin shiga tsakani a rikicin na Syria.

To domin tattauna wannan batun mun gayyato wasu baki da suka hada da:

Sheikh Usman Bari, tsohon jami'in Diplomasiyya na Ghana, kuma mai sharhi kan harkokin kasashen Larabawa; da Dr Uba Ahmed Ibrahim, malami a jami'ar Jos dake Najeriya.

Sannan mu na tare da Malam Nasir S. Rufai Sokoto, wani dan jarida da ke zaune a birnin Alkahira na Masar.

Akwai kuma wasu daga cikin masu saurarenmu dake kan layi, wadanda su ma ke son su bayyana ra'ayinsu.