Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Muhimmancin shari'ar Charles Taylor

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kusan mutane 50,000 ne suka rasa rayukansu a lokacin yakin

Kotun musamman da Majalisar Dinkin Duniya ke mara wa baya ta samu tsohon shugaban kasar Liberiya Charles Taylor, da hannu a munanan laifukkan da aka aikata a lokacin yakin basasar kasar Saliyo a shekarun 1990.

Kotun a birnin Hague, ta ce Mr Taylor ya taimaka, ta hanyar bada goyon baya ga kungiyar 'yan tawaye ta RUF, wajen cin zarafin bil'adama, da kisan kai, da fyade da kuma ta'addanci a lokacin yakin.

Sai dai alkalan kotun sun ce tasirin Mr Taylor a kan 'yan tawayen bai kai yadda har zai ba su umarni ba.

Amma dai sun ce a duka tuhumce-tuhumce 11 da ake ma shi, yana da hannu wajen taimakawa 'yan tawayen da kuma kitsa laifufukan yakin da suka aikata.

An dai dage shara'ar zuwa watan gobe lokacin da za a yanke masa hukunci.

Kamar wacce irin ta'asa ce aka aikata a lokacin yakin basasar? Menene muhimmancin wannan shari'a, da kuma wane irin tasiri za ta yi?

Wadanann sune abubuwan da za mu tatatunawa akan su a filin namu na ra'ayi Riga.

Daga cikin bakin da muka gayyato akwai; Malam Abubakar Kari na jami'ar Abuja, a Najeriya.

Da Comrade Shehu Sani Shugaban kungiyar Civil rights Congress take fafutukar kare 'yancin biladama a Najeriya.

Sai Jibrin Ibn Jibrin wani dan Najeriya dake koyarwa a Jami'ar Dooker Washington a Manrovia, Liberia.