Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yaki da cutar Polio a Afrika

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasashe uku ne kawai suka rage da cutar Polio a duniya

Hukumar lafiya ta Duniya ta soma gudanar da wani gangamin gaggawa dake da aniyar kawar da cutar Polio.

Yunkurin ya zo ne yayin da ministocin kiyon lafiya suka hallara a Geneva domin taron kiyon lafiya na duniya na shekara shekara, ta hanyar ayyana cutar ta Polio a matsayin wata annobar da ta shafi duniya baki daya.

Har yanzu dai Polio na ci gaba da kasancewa a kasashe uku, wato Nijeriya da Pakistan da kuma Afghanistan,to amma kwararru kan kiyon lafiya sun damu da bullar cutar a kasashen da a da suka kawar da ita.

To domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato baki da suka hada da:

Dr Mohammed Ali Pate, Minista a Ma'aikatar lafiya ta Najeriya da kuma Comrade Ibrahim Jibril, Shugaban Shirin kula da lafiya a matakin farko na kasa reshen Jihar Sokoto da Malam Rabi'u Musa, Jami'in hulda da jama'a na ofishin hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya -- UNICEF -- a wasu jihohin arewacin Najeriya.

Akwai kuma Aminu Tudun Wada, Shugaban Kungiyar mutanen da Cutar Shan Inna ta Polio ta Nakasa. Haka nan kuma ta wayar salula muna tare da wasu daga cikinku, ku, masu saurarenmu.