Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Hadarin jiragen sama a Najeriya

Image caption An yi haduran jiragen sama a Najeriya sau shida a shekaru goma da suka wuce

Bincike ya nuna cewar rayuka kusan dubu daya ne aka rasa a cikin shekaru goma da suka wuce sakamakon hadarin jiragen sama a Najeriya.

Alal misali, a shekarar 2002, wani jirgin saman kamfanin EAS ya fadi a jihar Kano, inda ya hallaka mutane 105 dake cikinsu da kuma karin wasu 74 da jirgin ya fado akan rukunin gidajensu.

Sai kuma ranar 22 ga watan Oktoban 2005, inda wani jirgin kamfanin Bellview ya fadi a jihar Ogun, kuma dukkan fasinjoji 117 dake cikin sa sun hallaka.

Wani Jirgin kamfanin Sosoliso ya fadi a ranar 10 ga watan Disambar 2005 a Fatakwal, inda ya kashe mutane 103 ciki hadda wasu daliban wata makarantar sakandare.

Har ila yau, Najeriya ta sake gamuwa da mummunan hadarin jirgin sama a ranar 17 ga watan Satumbar 2006, inda jirgin Dornier na rundunar sojojin sama ta kasar ya fadi a jihar Benue dauke da wasu manyan sojojin kasar, anan dai mutane 18 ne suka rasu.

Wani Jirgin kamfanin ADC ya fadi a ranar 29 ga watan Oktoban 2006, jim kadan bayan ya tashi daga filin saukar jiragen saman Abuja, kuma mutane 104 dake cikinsa duk sun rasu, hadda mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammed Maccido da kuma wasu 'yan majalisar dattijjai uku.

Sai na wannan makon, inda wani jirgin kamfanin Dana ya fadi a Lagos inda ya hallaka mutane 222, wato fasinjojinsa 153 da kuma mutane 69 wadanda jirgin ya fadi akan rukunin gidajensu.

Shin a ina matsalar take? Yaya kuke kallon yadda ake gudanar da harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya?

Wadanne matakai gwamnati ke dauka domin magance aukuwar irin wadannan haduran?

To domin tattauna wannan dama sauran batutuwa mun gayyato Senator Hadi Sirika, dan majalisar dattijai a Najeriya, kuma tsohon matukin jirgin sama wanda muke tare da shi ta waya a Kano.

Kyaftin Mukhtar Usman Shugaban hukumar binciken haduran jiragen sama a Najeriya wato Accident Investigation Bureau.

Da Kyaftin Muhammed Joji Sakatare Janar na kungiyar masu harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya, kuma shugaban kamfanin Sky Power Airways.

Da kuma wasu daga cikin masu sauraro da ke kan layin waya da kuma shafinmu na Facebook.