BBC navigation

Ko Wacce Tambaya da Amsarta

An sabunta: 6 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 13:17 GMT

Menene wannan?

Wannan wani shiri ne na gwaji wanda aka tsara da nufin ba ku damar tsinkayen yadda ake bayar da rahoto da kuma tattaunawa a kan gasar Olympics 2012 a Landan a shafin Twitter.

Wacce hanya kuka bi kuka zabo adireshi?

Mun zabo adireshi da dama na 'yan wasa daga sassa da dama na wasannin kasa-da-kasa. Mun yi jerin sunayen 'yan wasan tsere, da hukumomin Olympics, da marubuta labarin wasanni, da 'ya jarida, wadanda ke aikewa da sakwannin Twitter a-kai-a-kai, wadanda kuma ra'ayoyinsu za su kara armashi ga rahotannin da BBC ke bayarwa a kan Gasar Olympics.

Wanne irin bayani kuke bayarwa a shafin?

A mataki hudu ake gabatar da sakwannin Twitter.

Sakwanni na baya-baya: Wannan mataki na nuna sakwannin Twitter guda goma na baya-bayan nan daga adireshin mutanen da muka riga muka zaba.

Yayi: Wannan yana nuna muhimman kalmomin da mutanen da muke bi suka fi aikewa ta Twitter a sa'o'i 24 da suka gabata.

Adireshin intanet da aka fi musanyawa: Wannan yana nuna adireshin intanet din da mutanen da muke bi suka fi musanyawa a sa'o'i 24 da suka gabata.

Motsi ya fi Labewa: Wannan yana nuna su wadanda suka fi aikewa da sakwannin Twitter a cikin mutanne da muke bi a sa'o'i 24 da suka gabata.

Za kuma a rika sanya sakwannin Twitter na baya-bayan nan a cikin labaranmu masu dangantaka da Olympics da kuma rahotannin Olympics na musamman.

Shin ana tace sakwannin Twitter?

Ana tace dukkan sakwannin Twitter. Hakan na nufin za mu yi iya kokarinmu mu tace sakwannin Twitter bayan sun bayyana a shafin don tabbatar da cewa sun dace da ka'idojinmu [Link to house rules page]. Idan kuka ga wani adireshi da kuke tunanin ya saba da ka'idojinmu, ku yi amfani da shafinmu, Latsa Yadda ake Korafi, don jawo hankalin masu kula da sakwannin.

Yaushe wannan shafin ke aiki?

Shafin zai yi aiki ne tsakanin 22 ga watan Yuli da kuma 12 ga watan Agusta.

Za ku iya tuntubar mu ta gurbin da ke kasa:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.