Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ta yaya za a kauce wa ambaliyar ruwa a yankunanku?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar Pilato

Hukumar dake kula da nazarin yanayi a Najeriya wato NIMET ta yi gargadin cewa za a fuskanci ruwan sama mai karfin gaske a watannin Agusta zuwa Oktoba a sassa dabam-dabam na kasar.

Hukumar ta yi hasashen cewa yawan ruwan saman zai iya haddasa ambaliya, a jihohi goma sha biyar na Najeriya.

Irin wannan ambaliya dai kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi kamar yadda lamarin ya faru a jihohin Lagos, Plateau da Yobe da kuma Kebbi.

Shin wanne hali ake ciki a yankunanku? Kuma wadanne matakai ake dauka na shirya wa saukar ruwan saman, da kauce wa barnar ambaliyar?

Wasu kenen daga cikin abubuwan da muka tattauna a shirinmu na wannan makon: