BBC navigation

Ra'ayi Riga: Ta yaya za a kauce wa ambaliyar ruwa a yankunanku?

An sabunta: 10 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 21:35 GMT

Garmaho

Hukumar dake kula da nazarin yanayi a Najeriya wato NIMET ta yi gargadin cewa za a fuskanci ruwan sama mai karfin gaske a watannin Agusta zuwa Oktoba a sassa daban-dabam na kasar.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar Pilato

Barnar da ambaliyar ruwa ta yi a jihar Pilato

Hukumar dake kula da nazarin yanayi a Najeriya wato NIMET ta yi gargadin cewa za a fuskanci ruwan sama mai karfin gaske a watannin Agusta zuwa Oktoba a sassa dabam-dabam na kasar.

Hukumar ta yi hasashen cewa yawan ruwan saman zai iya haddasa ambaliya, a jihohi goma sha biyar na Najeriya.

Irin wannan ambaliya dai kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi kamar yadda lamarin ya faru a jihohin Lagos, Plateau da Yobe da kuma Kebbi.

Shin wanne hali ake ciki a yankunanku? Kuma wadanne matakai ake dauka na shirya wa saukar ruwan saman, da kauce wa barnar ambaliyar?

Wasu kenen daga cikin abubuwan da muka tattauna a shirinmu na wannan makon:

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.