Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Zaben Shugaban kasar Ghana

Al'ummar kasar Ghana su kusan miliyon 14 sun kada kuri'arsu domin zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki su 275 wadanda zasu shugabanci kasar tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Jam'iyyu takwas ne ke takarar kujerar shugabancin kasar, ciki har da shugaba mai ci a yanzu, wato John Dramani Mahama wanda ya dare kujerar mulki a watan Yulin da ya gabata sakamakon mutuwar tsohon shugaban kasar, John Atta-Mills.

Babban mai kalubalantar shugaban kasar sh ine, Nana Akufo Addo na babbar jam'iyyar adawa ta NPP.

Abinda ya fi jan hanakalin jama'ar kasar ta Ghana yayin wannan zabe shi ne, batun tattalin arziki, da karfafa tsarin demokuradiyya, saboda ana kallon Ghana a matsayin babbar abin misali ga sauran kasashen Afrika.

To ko yaya aka gudanar da zaben ? Kuma wane irin kalubale ne ke gaban shugaban kasar da za'a zaba?