Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zan tsaya takara a 2015 idan... —Buhari

Janar Buhari
Image caption Sau uku Janar Buhari yana tsaya wa takarar shugaban kasa

Dan takarar jam'iyyar CPC a shekara ta 2015 janar Muhammadu Buhari, ya ce zai iya tsayawa takara a zaben shekara ta 2015, idan har jam'iyyarsa ta nemi ya yi hakan.

Janar din ya bayyana haka ne a wata hira da wakilin BBC a Abuja Abdou Halilou lokacin da jam'iyyar ta CPC ta kaddamar da kwamitin ta da zai jagoranci tattaunawa da jam'iyyar ACN a yunkurin da jam'iyyun ke yi na kafa sabuwar babbar jam'iyyar adawa da za ta kalubalanci Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriyar.

Kwamitin dai na da makonni shida ne kan gudanar da wannan aiki.

Ya dai fara da bayyana ra'ayinsa kan yadda yake ganin batun hadakar na jam'iyyar CPC da ACN.