Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Karancin tsaftataccen ruwa a Afrika

Karancin tsaftataccen ruwa a Afrika
Image caption Miliyoyin mutane ne ke fama da karancin ingantaccen ruwa a Afrika

Wani rahoto da kungiyar fafutikar samar da ruwa ta WaterAid, ta fitar ya nuna cewa kimanin 'yan Afrika miliyan 210 ne ke fama da rashin tsaftar muhalli sakamakon karancin ruwa.

Rahoton ya ce gwamnatocin Afrika sun gaza cika alkawuran da suka dauka na samar da kudade domin tabbatar da tsaftar muhalli da kuma samar da ruwa ga al'umominsu.

Har ila yau rahotan ya jaddada kiyasin hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya mai cewa karancin ruwa da tsaftar muhalli na ciwa kasashen Afrika kudu da Sahara kusan kashi biyar cikin dari na abin da suke samu kowacce shekara.

Adadin ya haura kudaden agajin raya kasa da ake baiwa nahiyar ta Afrika.

Wani bincike da aka gudanar a shekara ta 2012, ya gano cewa kimanin yara 400, 000 'yan kasa da shekaru biyar na mutuwa kowace shekara sakamakon rashin tsaftataccen ruwan sha da tsaftataccen muhalli a nahiyar Afrika.

To shin ya matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha take a yankunanku? Kuma wadanne matakai suka kamata a dauka wajen magance wannan matsala ta karancin ruwa?

Wasu kenan daga cikin abubuwan da za mu tattauna a kansu a filin Ra'ayi Riga na wannan makon.

Kuma domin duba wannan batu mun gayyato mutane da dama da suka hada da Tanko Yusuf Arzuka, jami'in tsare-tsare na kungiyar WaterAid a Afrika, sai Muktari Shehu Shagari, mataimakin gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon ministan ruwa a Najeriya.

Akwai kuma Usman Dambaji, shugaban kungiyar da ke fafutukar samar da ruwa ga jama'a a jamhuriyar Nijar.

Sannan kuma akwai dinbim masu sauraranmu dake kan waya.