Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga; girke jiragen yaki marasa matuka a Nijar

Jirgi marsa matuki
Image caption Jirgi marsa matuki

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa, yanzu haka akwai jiragen saman yaki marasa matuka na Amurka a cikin kasar. Kakakin gwamnatin Nijar yace jiragen marasa matuka zasu taimaka wajen tattara bayanan tsaro.

Tuni dai shugaban Amurka, Barack Obama ya bayyana cewa Amurka ta aike dakaru dari zuwa Niger, kuma wadannan dakaru ne zasu yi aiki a sansanin jiragen saman yaki marasa matuka da Amurka ta kafa a Niger.

Amurka ta ce, jiragen saman marasa matuka zasu rika aikin tattara bayanan tsaro ne domin tallafawa dakarun Faransa da na kasashen Afurka wajen fatattakar 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama da ke yankunan arewacin Mali.

Sai dai kuma tun daga lokacin da Amurka ta kafa wannan sansani a Niger ne wasu ke bayyana fargaba, musamman ma bisa la'akari da yadda irin wadannan jirage suka rika hallaka jama'a bisa kuskure a kasashen Afghanistan da kuma Pakistan.

A wadannan kasashe lamarin har ya kai gwamnati ma da jama'a, a wasu lokutta na Allah-wadai da wadannan jirage marasa matuka.

Yanzu haka a Niger ma tuni wasu kungiyoyin farar hula suka fara yin Allah wadai da kafa sansanin Amurka a kasar, amma gwamnatin Niger din tana cewa, ganin irin abinda yake faruwa a Mali yasa ta dau wannan mataki.

Koda a makwabciyar Niger, wato Najeriya wasu na fargabar cewa, watakila nan gaba, ayukan jiragen yakin Amurkan marasa matuka na iya shafar kasar.